Mai sikila da ke son gina asibitin kula da masu larurar

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
Mai sikila da ke son gina asibitin kula da masu larurar

Aisha Ahmad Nakura mai larurar sikila ce wadda ta samu karfin gwiwar yin sana’ar sayar da kayan sawa duk kuwa da cewa jama’a na yi wa masu irin rashin lafiyarta kallon abin tausayi.

Sabanin masu irin wannan larura, Aisha ta ce kasancewar sau daya a shekara cutarta ke tashi ya sa ta sadaukar da sauran lokutan da take da lafiya wajen yin cinikayya.

Babban burin Aisha shi ne zamowa hamshakiyar attajira da za ta bude katafaren asibitin da za a rinka duba lafiyar masu cutar sikila.