Kusan diriricewa tayi, dan tayi mugun tsorata da ganinsa ga kuma mmki fal ranta dataga ya canja babu wannan qasumbar me yawa, yyi fresh dashi duk wanda ya ganshi bazaiyi zaton baida lpy ba.
            "Gashi"
taji ummi na mgn a bayanta. Adan kunyace ta juyo sbd ta tarar ta tana karewa mijinta kallo.
Basarwa ummi tayi bata nuna ta ganta ba, tace,
              "ga kujera ki zauna"
tayi mgnr tana zama itama. Zama jamilan tayi ta zubawa ummi ido tace,
                "wai ya naga abubuwa haka?"
Ummi tace,
               "kamar ya fa?"
               "Uhum yadda lbri yake zuwane ba haka na gani ba"
ummi tayi murmushi tace,
                "kinsan shi lbri idan za'a bayar dadine dashi mutum be sanin sanda zai kara mai gishiri."
Jamila ta tabe baki itafa ba yanda taso gani ba kenan, can tace,
               "kuma haka kike ta fama da wannan garjejen qaton a gida?" Ummi tace,
               "ban fahimceki ba?"
             "Toh ai gani nayi ba hankali har kika iya jure kashi da fitsarin sa" rintse ido ummi tayi tana tunanin yadda mutane suka kasa fahimtar El-bash yanda kasan A/C haka yake a waje zafi a ciki sanyi fahimtar da tayi masa kenan adan zamanta dashi. Yyinda jamila ta samu damar juyawa gefen El-bash tana kare masa kallo musamman data ga ya lumshe ido, tana ayyanawa a ranta inama ita aka bawa mahaukacin dan kallon fuskar sa kadai ya isa a zauna dashi.

Ummi na bude ta sake kama jamila na kallon el-bash, wani irin abu taji yazo ya tokare mata kirji da sauri tace,
              "jamila tashi muje dakina ki gani ranar da kukazo babu dama."
Dan yatsina fuska jamilan tayi bataso ta musa ummi ta gane asirin zuciyar ta dan haka tabi bayanta tana dan juyowa ta kalleshi a sace.

Yini jamila tayi a gidan koda taje dakin ma kasa zama tayi dan haka tace zata sauka kasa, ganin haka ummi ta riko hannun el-bash ta maida shi daki tana fita kuwa yyi dariya yanajin dadi a ransa ashe ummi na sonsa haka? Tunda ya hango kishi a idonta, takaicine ya kama jamila tace tafiya zatayi, ummi kuwa ta hado mata sha tara ta arziki,  har bakin gate ta raka ta, lkcn mlm sabo na zaune ummi ta matsa ta gaishe shi ya amsa mata sama2 babu sakin fuska kamar kullum, a sanyaye tabar gun tanajin wani iri a ranta,yyinda jamila tayi tafiyarta gida wani daci na taso mata arai, duk yadda za'a sai an aura mata El-bash ai ba cikinsu daya da ummin ba kazalika ba ubansu daya ba ehe. Haka tayi ta sakawa da warwarewa harta isa gida.


~~~~~~
Bayan kwana biyu, suraj ya kawo musu ziyara gidan shi da wata yarinya wacce bazata wuce sa'ar ummin ba anace da ita Aisha, lkcn ummi suna parlo tana kallo ta juya taga el-bash ya zubama kallon ido, sai taji ya bata tausayi a tunanin ta ita kadai keyi batasan kuwa shima kallon yake kamar ita. Suna hakan suraj sukazo, ummi da fara'a ta tarbesu shima el-bash murmushi yake batare da yace komai ba, kusa dashi suraj ya zauna ita kuma yarinyar me suna Aisha ta zauna kusa da ummi suna gaisawa, ummi tace,
              "oh sai yau suraj aka kawo min aysha" aysha tayi dariya tace,
             "kuma lefin shi ne" suraj yana dariyar shima yace,
             "au hademin kai zakuyi dan na hada ku?" Ummi tace,
             "ai gskyne"
suraj ya kama hannun El-bash yace,
              "bari naja abokina muje baya muma mu hada kai".
dariya sukayi masa a tare sukace,
                "kodai zancen kurame ba"
dariya el-bash yyi sbd ya juya musu baya bazasu ganshi ba, suraj yace,
             "hakan ma yafi dadi ya zuramin ido na gwalala masa ido"
daria suka sake yi masa be kara cewa komai ba sukabi ta corridor din kitchen inda zai sada su da garden din part din.

Suna tafiya Aysha tace,
               "ummi ko awaya bakya nemana, inason nazo gunki wlh toh abubuwan ne sai a slow yanzun ma dan kince nazo na miki kitso ne" ummi tace,
              "kinsan ba waya a hannu na, idan na rikema wazan kira tunda kullum muna tare"
cikin tausayi aysha tace,
            "Allah ya bashi lpy"
            "Ameen" ummi ta amsa tana fadin kafin su dawo,
             "kama min kan nawa wlh tunda nayi auren nan bega kitso ba" aysha ta cire gyalenta tace,
              "kawo kayan kitson nayi miki ko shida ne"
ummi ta haura sama ta kawo nan aysha ta dinga mata kitson sharp2 ta gama. Ummi ta tashi tace,
              "kai gsky ya kamata ki bude saloon aysha"
aysha tace,
                 "koh?"
              "Ehmana kitson masha Allah"
ummi ta fada tana shafa kai.

*Wacece Aysha?*
Aysha Yusuf budurwar Suraj ce wanda ake shirye-shiryen bikinsu nan da dan wani lkci, da tuni ma anyi bikin suraj ya roki Alfarma a kara masa lkci sbd aikin da suke gudanarwa musamman na a mutu ne ko ayi rai?? Yana gamawa za'a sha bikinsa, to el-bash ma haka yaso idan sun gama ya nemi macen aure sai gashi auren yazo masa yna tsaka da aiki to dama haka Allah ke ikonsa kana naka ne yana nasa kuma nasan shine daidai. Suraj da yawan lokuta idan yazo yana hada ummi da aysha a waya har sukayi sabo kamar sunsan juna, mutunci ne me tsafta ya kullu a tsakanin su.

••√√√
Suraj ya kalli El-bash yace,
         "jibi ne fah"
          "Insha Allah" El-bash ya fada yanajin kamar ya jawo jibin tazo kusa, suraj yace,
           "ya naga sai doki kke ko akwai wani abune?"
Dan murmushi El-bash yyi ya rike kirjinsa saitin zuciyar sa yace,
            "nan wajen ya kosa ya fitar da abinda ke ciki" da mmki suraj yace,
             "kai nifa ban gane ba"
El-bash ya harareshi yace,
             "Ummina mana na kosa na sanar mata *ABINDA KE RAINA* i so much love her" 
yyi mgnr yana lumshe ido yanaji a ransa inama ummin ya furtawa hakan, wata irin dariyar shakiyanci suraj yyi yana rike ciki yace,
            "Gske kke kuwa?" Bude ido el-bash yyi yana murmushi, suraj murna ta kama shi dan bayaso ummi tasha wahalar banza, cikin tsokana yace,
              "but when? How? Little ce fah."
El-bash yce,
              "toh sai kayi kuma kaifa iskancin ka nada yawa mtwss"
dariya suraj ya sake yi yace,
                "haba maida wuqar ai dole na tayaka murna yanzu ka shigo system din"
               "toh sharukhan uban soyayya"
El-bash ya fada yana hararar sa, suraj yace,
              "haba waneni ai ka wuce tunani na yanzu ni dan kallo ne"
El-bash yace,
                "kaga mu koma bangaren aiki."
Nan suka fara lissafin yadda zasu kasance a wajen.


°°°°°
A daren ranar haj suwaiba ta gama tsara yadda zasu dauke ummi, duk wani shirinta ta gama tsaf.

Yyinda a bangaren ummi haka kawai ta dinga jin faduwar gaba, tun safe takejin haka saidai faduwar gaban be tsananta ba kamar yanzu da dare yyi, harta kwanta ta mike dan a dakin el-bash take, batason tashin sa ta fita a hankali lkcn besan da fitar ta ba sbd bcci yake, ummi dakinta taje tayo Alwala sbd bugun qirjinta ya tsananta, ji take kamar akwai abinda zai sameta me muni dan haka ta kabbara sallah dan kai kukan ta wajen Rabbi,

kusan kwana tayi tana sallah hade da tilawar Qur'an duk wata addu'a data sani ba wacce bata karanta ba, ummi har asuba taje a takaice dai bata iyayin bcci a ranar ba, anan dakinta tayi sallah idonta duk ya kekashe babu alamun bcci jikinta yyi sanyi kalau.

El-bash be farka ba sai asuba anan yaga ummi bata nan, zaton sa toilet taje yaji ba motsi nan yasa a ransa kila dakinta taje dan haka shima ya fada toilet danyin Alwala.

Koda ummi tayi asuba bata fasa Addu'ah ba hankalin ta ya tashi sbd matsanancin faduwar gaba da takeji, sam bazata iya bcci ba da rana ta fito ta tashi ta gyara daki, bayan ta gama ta leka dakin el-bash taga yana bcci jawo kofar tayi ta gangara kasa, nan ta gyara parlon tsaf taje tayi musu breakfast tana tsaka da jera abincin ya sakko, murmushi tayi shima ya maida mata da murmushin yana wara mata hannu, zuwa tayi ta fada kirjinsa ya rungume ta yana kissing dinta. A haka suka karasa kujera ta jawo musu abincin.

Saida suka gama cin abincin taji wani irin nannauyan bcci yazo mata, kan kujera ta koma ta kwanta dan batajin zata koma sama dan idonta yyi nauyi. El-bash ganin ta kwanta ya gyara mata kwanciyar sannan ya haura sama sbd aikin da zasuyi gobe yana bukatar shiri mekyau.

Barinsa wajen keda wuya aka turo kofar parlon a hankali, ummi ta manta bata rufe ba, dan haka aka samu damar shigowa, mutum biyune masu shigowar kowa ya rufe fuska, haj suwaiba ce da erta sakina, wani farincikine ya kamasu da alama bazasu wahala ba, cikin sauri haj suwaiba ta ciro farin kyalle ta manna a hancin ummi, batare da bata lkci ba suka sungumi ummi wacce ta zama kamar gawa, har cikin mota suka ajeta,

lkcn haj suwaiba ta aiki mlm sabo badan tana bukatar aikan ba saidan bataso ya gani tunda ya hada dangantaka da ummi, sakina ta koma part dinsu da sauri yyinda haj suwaiba ta fice da ummi a tamanin.

El-bash besan wainar da ake toyawa ba saima yana aikine a jima yyi murmushi sbd gab yake daya balle zuciyarsa dan gayama abar kaunar sa ummi abinda ke ciki, jawo wayarsa yyi ya kalli hoton ummi daya dauka tana bcci, wayar yakai bakinsa yyi kssn dinta yana mannawa a kirji zazzafar soyayyar ummi na ninkuwa a ransa.

EL-BASHEERWhere stories live. Discover now