Ana zaben raba gardama kan amfani da manyan kudi a India
Al’ummar India yau na zabe da ake kallo a matsayin na raba gardama kan shirin Firaiminista Narendra Modi na hana amfani da manyan takardun kudi a wani mataki na hana manyan attajirai kaucewa biyan kudin haraji.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Zaben na yau zai kasance tamkar minzanin gwajin farin jinin Firaiminista Nerendra Modi wanda ke a wa’adin mulkinsa na farko.
An gudanar da zaben ne a jahar Uttar Pradesh mai jama’a da suka zarta miliyan dari biyu, Jahar da sakamakon kuri’u ke da matukar mahinmanci a zabukan India.
Firaiministan Modi na son ganin shirin nasa na haramta amfani da manyan takardun kudi ya sami karbuwa don magance matsalar da ta shafi manyan attajirai da ke kaucewa biyan kudin haraji al'amarin da ke matukar yin nakasu ga tattalin arzikin India.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu